MUHAMMAD SA’AD ABUBAKAR III
SARKIN MUSULMIN NAJERIYA

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya ce akwai bukatar a yi taka -tsantsan wajen daukar sabbin jami’an tsaro domin gudun dauki marasa tarbiyya.

Sa’ad Abubakar ya ba da wannan shawarar ce a taron da aka gudanar kan harkokin tsaro wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya, da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sokoto da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce daukar sabbin jami’an tsaron na da matukar muhimmanci, kuma zai taimaka matuka wajen samar da tsaro musamman a wuraren da ‘yan ta’adda ke cin karansu babu babbaka.

Mai Alfarman ya kuma bukaci sarakuna su hada kai da jami’an tsaro wajen tabbatar da an samu nasara a yaki da ake yi da ‘yan ta’adda a jihar da kasa baki daya.
Haka kuma, gamayyar kungiyoyin matasa a jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da shugabannin daliban yankin, sun bukaci hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen samar da tsaro a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *