Shugaban rundunar sojojin Nijeriya Janar Abayomi Olanisakin ya bukaci ‘yan Nijeriya su ba jami’an soji hadin kai a yaki da su ke da ayyukan ta’addanci a shiyyar Arewa maso yamma.

Olanisakin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke kaddamar da wasu aikace-aikace da shelkwatar tsaron Nijeriya ta gudanar a wasu kananan hukumomi da ke Katsina.

Shugaban wanda ya samu wakilcin kwamandan rundunar soji ta 8 da ke jihar Sokoto Janar Aminu Bande, ya ce shelkwatar tsaro ya gudanar da aikace aikacen ne domin samar da ababen more rayuwa da kuma inganta rayuwar al’ummar yankunan.

Aikace aikacen dai, sun hada da rijiyoyin burtsatse a garuruwan Rahamawa da Tudun Matawalle da Tudun Natsinta duk a jihar Katsina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *