Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta nuna damuwa kan yadda ake samun hukunce-hukuncen kotu da ke cin karo da juna gabannin zabukkan jihohin Edo da Ondo.

Kwamishinan sashen yada labarai da wayar da kai ha hukumar Festus Okoye ya bayyana haka a wani taron da suka gudanar.

Ya ce wasu umurnin da kotu suka bada ba su shafi wuraren da aka samu matsaloli da ya kamata a dauki matakai gabannin zaben ba.

Sannan ya ce hukumar ta cimma matsaya a kan zaben maye gurbin dan majalisar da ke wakiltar Nasarawa ta tsakiya da ya rasa ransa, kuma za a gudanar da zaben ne a ranar 8 ga watan Augusta.
Okoye, ya ce sanarwar a hukumance za ta fita a ranar 29 ga watan nan da muke ciki, sannan hukumar ta bukaci jam’iyyu su gudanar da zaben fidda gwanin su tsakanin ranakun 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli mai kamawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *