Sunansa na barazana da baje kolin arziki a shafukan sada zumunta shine ‘Hushpuppi’, a matsayin hamshakin dan kasuwa daga Najeriya mazaunin kasar Dubai.

Daga Wakilinmu a Dubai.

Daya daga hotunan Hushpuppi a Instagram

‘Yan sandan kasar Dubai ne suka jefa wannan dan taliki cikin komarsu bayan shafe watanni hudu suna bincike a kansa ta hanyar kaddamar da shirin farautar Dan Najeriyar da aka fi sani da suna ‘Hushpuppi’ a shafukan sada zumunta. ‘Yan sandan hadaddiyar daular larabawan su ke zargi da aikata ayyukan damfara a cikin kasar da wajenta da sunan shi dan kasuwa ne mazaunin Dubai.

Tsarin farautarsa da ‘yan sandan suka wa lakabi da ‘Farautar Dila na 2’ ya kama gawurtaccen a cikin samame har shida, tare da kame wasu ‘yan tawagarsa da ake zargi da taya shi damfarar har mutum goma sha biyu, ciki har da wani Olalekan ponke da ake wa lakabi da ‘Woodberry’.

Ana dai zargin mai takamar cewa shi hamshakin dan kasuwar ne da aikata laifuffukan damfara ga mutane daban daban a kasashen duniya. Sannan yayi suna sosai wajen nuna alfahari da kudi da kayan alatu a shafinsa na Instagram.

Daya daga hotunan Hushpuppi a Instagram

Kadan daga ayyukan su Ramoni sun hada da yin utse a shafukan hada-hadar kudi tare da canza akalar kudaden zuwa bankunan kashin kansu maimakon na kamfanonin da aka yi hudar ciniki da su.

Kirkirar sakonnin imel din jabu don karkatar canji da aiken kudade daga jama’a da bankuna zuwa na su asusun ajiyar kansu. Misali idan wani ya sayi abu ta yanar gizo ya biya kudinsa, sai kawai kudin su fada asusun su Hushpuppi maimakon idan aka sayi kayan.

An kuma gano cewa akalla mutane kusan miliyan biyu ne suka fada tarkon Hushpuppy da tawagarsa. Sannan sun damfaridin da ake zargin sun haura Naira Biliyan 168 idan aka canza daga kudin kasar na dirham zuwa kudin Najeriya.

‘Yan sandan sun kuma kwace kayayyakin da kudinsu ta haura dirhami miliyan 150 daga wannan tawagar damfara. Sai kuma na’urar kwamfuta guda 21, wayoyin hannu guda 47, hade da wasu manyan rumbun kwamfuta guda 15 da kanana guda 5 duk a lokacin samamen na farautar Dila.

Daya daga hotunan Hushpuppi a Instagram

Sannan an karbi motocin alfarmar da Ramoni da mukarrabansa suka siya da kudin damfara wanda kudin motocin ya kai kimanin dirhami miliyan 25 kwatankwacin sama da naira biliyan 2 a kudin Najeriya. Zuwa yanzu dai ba a kai ga samun labarin gurfanar da su Hushpuppi a gaban kotu ba.

Haifaffen Najeriya ne da aka haifa a shekarar 1988 ya kuma girma a jihar Legas. Sannan yana fankamar cewa shi dan kasuwa ne mai harkar saye da sayarwa da kuma gine-ginen gidaje a fadin duniya musamman inda ya ke zaune wato kasar Dubai.

Cikakken sunansa kuma na ainihi Ramony Igbalode amma ‘yan sandan hadaddiyar daular labarawan sun gano yana da wani suna Ramon Olurunwa Abbas da ya ke amfani da shi wajen damfarar jama’a ta yanar gizo Kamar yadda ‘yan sandan na Dubai suke zarginsa.

Shiga shafinsa na Instagram ta nan don ganin irin rayuwarsa a idon duniya:

https://www.instagram.com/hushpuppi/

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *