Ministan kula da harkokin zuba jari da masana’antu Adeniyi Adebayo, ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da ayyukan yi kimanin milliyan 5 a shirin ta na farfado da tattalin arzikin nijeriya bayan annobar Coronvirus.

Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Julius Toba-Jegede a Abuja.

Ministan ya ce, akwai shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke da shi na kubutar da wasu ‘yan Nijeriya milliyan daya da dubu dari 4 daga rasa ayyuka.

Ya ce shirin wanda ya fito ta karkashin ma’aikatar sa, zai maida hankali ne wajen taimakawa kanana da matsakaitan masana’antu a lokacin annobar COVID-19 da kuma bayan kawo karshen cutar a Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *