Hukumar hana fasa kwabri ta kasa Kwastom ta samar da kudaden shiga kimanin naira billiyan dari 5 da miliyan 73 a tsakanin watannin Janairu zuwa Mayu, daga cikin naira billiyan dari 9 da miliyan 57 da ta yi hasashen samu a shekara ta 2020.

Shugaban hukumar Hameed Ali ya sanar da haka a lokacin da ya ke tattaunawa da kwamitin kula da harkokin hukumar na majalisar dattawa a Abuja.

Hameed Ali wanda ya samu wakilcin mataimakin kwantrola  da ke kula da sashen gudanarwa Sani Umar, ya ce hukumar ta cimma fiye da kaso 50 cikin dari na kudaden da ta yi hasashen samu a wannan shekarar.

Da ya ke amsa tambayoyin kwamitin a kan rashin sa kudaden a asusun gwamnatin tarayya, shugaban hukumar ya ce ba wani kayyadedden lokaci da hukumar ta ke da shi na sanya kudaden da ba a yi amfani da su ba a asusun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *