Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya ce rikicin jam’iyyar APC ta ‘yan Najeriya ce.

Lawan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Dan majalisar ya ce sun tattauna da shugaba Buhari kan tabarbarewar tsaro musamman a yankin Arewacin Nijeriya, kuma ya shaida wa shugaban halin da ake ciki da kiraye-kirayen da wasu ke yi saboda matsin da su ka fada saboda rashin tsaro.

Ya ce lokaci ya yi da ya zama wajibi manyan hafsoshin tsaro su jajirce wajen kawo karshen matsalar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *