Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya, ta ce za ta tattauna a ranar Talata kan mataki na gaba da za ta ɗauka, bayan kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da aikin hajjin bana ga maniyyatan ƙetare.

Hukumar ta ce duk da shawarwarin hukumomin Saudiyya na a dakatar da shirye-shiryen aikin hajjin bana, an cigaba da wasu shirye-shiryen ibadar a Najeriya.

Hukumar ta kara da cewa, tun farko ba su so a ce su daina shirye-shiryen kwata-kwata ba, don gudun daga baya a ce za a yi aikin hajji.

Kwamishinan ayyuka na hukumar Abdullahi Magaji Harɗawa, ya ce matakin Saudiyya bai zo masu da mamaki ba, duk da ya ke sun shafe tsawon watanni a cikin zullumi.

Ya ce ko da ya ke su ba su kai ga yanke hukunci ba, amma ganin wasu ƙasashe sun fara bayyana aniyar su ta janyewa daga halartar aikin hajjin su ma tuni sun fara yunƙurin sanin abin yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *