Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa, game da matakin da gwamnatin jihar Oyo ta dauka na sake bude makarantu daga ranar Litinin, 29 ga watan Yuni.

Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce matakin na bude makarantu a wannan yanayi da hali da ake ciki ya yaki da cutar korona babban kuskure ne.

Nwajiuba ya ce shawarar da gwamnatin jihar Oyo ta yanke za ta iya sa a samu karuwar adadin mutanen da cutar korona za ta harba a jihar.

Alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC dai sun bayyana jihar Oyo a matsayin ta hudu cikin jerin jihohin da su ka fi kamuwa da cutar korona a fadin Nijeriya.

Ministan ya bayyana damuwar ne, yayin taron kwana guda-guda da kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ke shiryawa a Abuja.

Tuni dai gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya fitar da tsare-tsaren sake bude makarantu da nufin ba dalibai damar komawa domin su cigaba da daukan darasi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *