Rundunar Sojin saman ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Hadarin Daji sun kai wa ‘yan bindiga hare-hare ta sama a jihohin Katsina da Zamfara.

Babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Manjo Janar John Eneche ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kai hare-haren ne domin fatattakar ‘yan bindigar a yankin.

Eneche ya ce, jami’an sojin sun yi amfani da bayanan sirrin da suka tattara wajen zakulo maboyar tsagerun domin karya lagonsu.

Ya ce  sojojin suka kai hare-haren ne Dutsen Asolo da Birnin Kogo da ke jihar Katsina da kuma sansanin Dogo Gede da ke Dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *