Babbar kotun tarayya dake Fatakwal ta ba Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki damar tsayawa takara a jam’iyyar PDP.

Kotun ta yi watsi da karar da daya daga cikin yan takaran kujeran gwamnan jihar, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shigar.

Alkalin kotun Emmanuel Obile ne yanke hukuncin bayan dukkan bangarorin biyu sun yi sulhu tsakaninsu kuma wanda ya shigar da karar ya janye kararsa.

Mai ba jam’iyyar PDP shawara kan harkokin shari’a, Emmanuel Enoidem, ya ce janye karar da Omoregie Ogbeide-Ihama yayi ya sa Alkalin yayi watsi da karar.

Ya ce yanzu babu abinda zai hana gwamna Obaseki takara a zaben fidda gwanin da zai gudana gobe Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *