Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Victor Giadom ne halastaccen shugaban riko na jam’iyyar APC.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter.

Ya ce matakin da shugaba Buhari ya dauki ya biyo bayan tattaunawa da ya yi da masana harkokin shari’a.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari zai halarci taron da Giadom ya kira gobe Alhamis, ta fasahar zamani, kuma ana sa ran gwamnonin jam’iyyar da shugabannin majalisar dokoki za su halarta.

Sannan ya gargadi kafofin yada labarai su guji yada cewa APC na cikin rikici.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *