Kwamitin kula da masallacin Jumma’a na Miyetti dake jihar Gombe a arewacin Najeriya, ya dakatar da shahararran malamin Addinin Musuluncin nan, da ake kira Albanin Gombe daga limanci a masallacin.

Kwamitin ya dakatar da malamin ne sakamakon zage-zage da kushe manyan mutane a duk lokacin da yake gudanar da wa’azi ko huduba a lokacin Sallar Juma’a, wanda a cewar kwamitin ya saba ka’idojin Masallacin.

Albanin Gombe dai ya yi kaurin suna wajan zagin Gwamnatin tarayya, na jihohi kan halin matsin rayuwa da ake ciki, inda yake ta fafutukar ganin gwamnati ta sassautawa al’umma.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *