Manyan hafsoshin tsaro da jami’an tsaron leken asiri sun gana domin fito da sabbin dabarun tunkarar matsalolin ta’addanci da suka addabi wasu yankuna a Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’in yada labarai da hulda da jama’a a shelkwatar tsaro dake Abuja.

Eneche ya ce ganawar da shugaban sojin kasa Gabriel Olanisakin ya jagoranta ya maida hankali ne kan hanyoyin da jami’an tsaro za su hada kai tare da fito da sabbin dabarun yaki da ta’addanci.  

Ya ce taron ya cimma matsaya kan sabbin dabaru da jami’an tsaron za su rika bi wajen yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi yankin arewacin Najeriya musamman ma Arewa maso yamma.

Eneche ya ce jami’an tsaro na neman hadin kan ‘yan Najeriya musamman ma da bayanan sirri wajen magance matsalolin tsaro dake addabarsu cikin gaggawa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban hafsoshin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, Shugaban sojin ruwa Vice Admiral Ibok Ete Ibas, shugaban sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar, da babban sufetan ‘yan sanda Adamu Muhammad.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *