Godwin Obaseki
Gwamnan Edo

Babbar kotun tarayya  dake Fatakwal babban birnin jihar Rivers ta hana Godwin Obaseki tsayawa takarar fidda-gwani na tsayawa takarar gwamna da jam’iyyar PDP za ta gudanar.

Obaseki ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne bayan jam’iyyar APC ta hana shi sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu a karkashinta.

A baya dai jam’iyyar PDP ta ba Obaseki damar shiga cikin zaben fidda gwani da ta shirya kuma zai gudana a ranar Alhamis ne dai za a yi zaben fidda gwanin.

Sai dai wani dan takara daga cikin masu neman tsayawa a jam’iyyar Omoregie Ihama, ya garzaya kotu ya nemi a hana Obaseki tsayawa, saboda a cewar sa, bai sayi fam ba, kuma lokacin da ya koma jam’iyyar PDP, an rigaya an rufe lokacin sayen fam na takara.

Sannan kuma Ihame ya ce sai wanda wanda ya sayi fam zai iya tsayawa takara, sannan kuma ya shaida wa kotu cewa ya na tababar takardun makarantar Obaseki.

Kuma kotun ta dakatar da Obaseki, har zuwa a ga hukuncin da za ta yanke a gobe Laraba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *