Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari garin Ruwan Tofa dake ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutum 21 ne suka mutu sakamakon harin ‘yan fashin dajin suka kai a garin.

Wasu shaidun gani da ido sun ce mahara fiye da 200 ne suka auka wa garin a kan babura tare da buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi, biyo bayan yunkurin da mazauna garin suka yi na yin fito na fito da su.

Sun ce daga cikin mutanen da aka kashe har da wata mace ɗaya, da kuma maza 20, yayin da aka jikkata ƙarin mutane goma sha biyar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce zuwa yanzu ta tabbatar da mutuwar mutane goma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *