Mahukuntan kasar Saudi Arabia sun soke aiki hajjin bana na shekarar nan da mu ke ciki ta 2020. Wacce ta yi daidai da shekarar Musulunci ta 1441 bayan hijira.

Matakin ya bayyana cewa tsirarin ‘yan asalin kasar da kuma ‘yan wasu kasashen waje da ke zaune a cikin kasar ne kadai za su yi aikin hajjin bana amma ba tare da dimbin alhazan sauran kasashen duniya ba sakamakon cutar Corona.

Ma’aikatar ayyukan haji da umra ta kasar sun dade suna ta zaman tattaunawar yadda za su bullo wa lamarin hajjin na bana, wanda a yanzu suka sami matsayar dakatar da shigar alhazan kasashen duniya da miliyoyin jama’a ke tururuwar shiga cikin kasar don sauke farali.

Ra’ayoyi 2

Your email address will not be published. Required fields are marked *