Babban Hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bukaci manyan jami’an soji su kara tashi tsaye wajen yaki da ayyukan ta’addanci da suka addabi kasar nan.

Mai rikon mukamin daraktan yada labarai na rundunar sojin Sagir Musa ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan taron da Buratai ya yi da manyan jami’an sojin.

Buratai ya ce an shirya taron ne domin ankarar da jami’an sojin kan bukatar da take akwai na su tashi haikan wajen yakar kungiyar Boko Haram da kuma ‘yan ta’addan da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Ya ce taron ya maida hankali ne akan matsalolin tsaro da kuma bukatar da take akwai na fito da sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sannan ya umurci dukkanin manyan jami’an da su tabbatar sun bi umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *