Shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ne ya karyata labarin da a ke yadawa na cewa ma’aikatan KAROTA sun yi fada da ‘Yan Sanda ne yasa suka kasa fita aiki a yau
Baffa Babba Dan Agundi, shugaban KAROTA
Hoto: KAROTA/Facebook

A cikin wata sanarwar muryar da ya fitar ga manema labarai da kafafen sada zumunta, Shugaban na KAROTA Baffa Babba Dan Agundi ya ce jita-jitar cewa dogarawan hanyar na jihar sun yi fada da jami’an ‘yan sanda ne ya sa suka ki fita aiki ba yau ba gaskiya ba ce.

Ya bayyana rashin fitowar ma’aikatansu na da nasaba da barazanar kai harin da ‘yan bindiga suka yi wa jami’an nasu. Amma ya tabbatar da cewa suna aiki ka-in da na’in da hukumar ‘yan sandan jihar Kano Wadanda a yau su suka aiwatar da aikin ‘yan KAROTA na bada hannu da kuma ganin yadda za su bullo wa lamarin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *