YEMI OSINBAJO
MATAIMAKIN SHUGABAN NAJERIYA

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce a shirye ‘yan Najeriya suke su rika biyan kudin wuta idan kamfanonin rarraba wutar lantarki suka inganta yadda suke rabata ga al’umma.

Mataimakin shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi na wani taron hanyoyin farfado da tattalin arziki bayan yakar annobar korona.

Ya ce ba gaskiya bane maganar cewa ‘yan Najeriya bas a son biyan kudin wuta yadda ya kamata, ya ce hakan na faruwa ne kawai saboda gazawar kamfanonin na bada isashen wutar lantarki.

Osinbajo ya ce akwai bukatar kamfanonin su inganta harkokin wutar lantarki a Najeriya duk da cewa hakan na faruwa ne sakamakon rashin bin hanyoyin da suka kamata wajen cefanantar da bangaren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *