Hukumar yaki da masu safarar bil’adama ta Najeriya NAPTIP ta rufe shelkwatar ta dake Abuja na tsawon makwanni biyu sakamakon barazanar bullar cutar korona.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun babban jami’ar sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Stella Nezan.

Shugabar hukumar ta kasa Dame Julie Okah-Donli, ta bada umurnin inda ta bukaci jami’an dake aiki a wuraren da abin bai shafa ba da su tafi hutun mako guda, domin bada damar yin feshin magani.  

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun tabbatar da cewa wasu jami’an hukumar biyu sun yi mu’amala da wata mata da ake kyautata zaton cutar korona ya kashe ta.  

Okah-Donli, ta ce za a yiwa dukkanin jami’an hukumar dake aiki a sakatariyar gwajin cutar ta korona, kafin su koma bakin aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *