Ministan kula da harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya yi Allah wadai da hare-hare biyu da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai a ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar Ghana.

Ministan wanda ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce abin takaici ne kwarai da gaske.

Ya ce gwamnatin tarayya na tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta mika bukatar daukar matakin gaggawa domin gano mutanen da suka kai harin.

Gwamnatin tarayya ta kuma bukaci a ba da cikakken tsaro ga ‘yan Najeriya da kadarorinsu da ke kasar ta Ghana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *