Gwamnatin jihar Borno ta dauki jami’an tsaron sa kai dubu 12 da dari 7 da 35 da suka hada da mafarauta domin kara karfafa aikin jami’an tsaro na yaki da ayyukan ta’addanci a jihar.

Kwamishinan kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar Sugun Mai-Mele, ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske kan aikace-aikacen ma’aikatar na tsawon shekara guda da ta gabata.

Ya ce gwamnatin jihar za ta rika kashe naira milliyan dari da 31 da dubu dari 9 wajen biyan wadanda ta dauka domin tsaron kananan hukumomi 25 dake fadin jihar.

Kwamishinan ya ce a tsakankanin lokacin ma’aikatarsa ta gyara fadar masarautun Shehun Dikwa da na Bama da a baya ‘yan ta’addan Boko Haram suka lalata.

Sannan gwamnatin jihar ta samar da tan dubu 3 na takin zamani da trakto guda dari da 34 domin inganta harkokin noma a kauyakun dake yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *