YEMI OSINBAJO
MATAIMAKIN SHUGABAN KASA

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya ce ya kamata a sake zama tare da tattaunawa akan kudaden da ake kashewa akan manyan jami’an gwamnatin Najeriya.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a taron da wani Coci ya shirya kan hanyoyin farfado tattalin arzikin Najeriya, bayan yakar annobar cutar korona.

Osinbajo ya ce duk da cewa hakan zai kasance mai wahalar gaske, saboda wadanda za su yi gyaran na amfana da tsarin, amma ya zama wajibi a san na yi.

Ya ce a yanzu kashi 70 cikin dari  na kudin shiga da ake samu a Najeriyana tafiya ne wajen biyan alawus-alawus, wanda duk mai hankali ya san akwai bukatar a rage.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *