YEMI OSINBAJO
MATAIMAKIN SHUGABAN NAJERIYA

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce cin zarafin jinsi, fyade da sauran wasu laifukka makamantan haka na kara ragewa ‘yan Najeriya da kasan kanta daraja.

Osinbajo ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron hukumar kare hakkin bil’adama ta shirya ta fasahar zamani kan yawan aukuwar cin zarafin jinsi a Najeriya.

Osinbajo a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Laolu Akande, ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da yakar cin zarafi ta hanyar amfani da kwamitin farfado da tattalin arziki na johohi da tarayya.

Sannan ya yabawa hukumar bisa jagorantar tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a magance matsalar cin zarafin jinsi da ta addabi Najeriya, da kuma gangamin da ta yi ta shiryawa.

Sannan ya yabawa minister kulada da harkokin mata da ci gaba Paulen Talen na jawabai masu muhimmanci da ta gabatarwa taron majalisar zartaswa ta tarayya da ta kai ga daukar wasu muhimman matakai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *