Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta ce akwai barazanar kara samun mai dauke da cutar shan inna a Najeriya a daidai lokacin da take jiran hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana ta a matsayin wacce ta yaki cutar baki daya a watan Augusta.

Shugaban hukumar Faisal Shuaib ya bayyana haka a lokacin tattaunawa ta fasahar zamani da aka shirya da masu ruwa da tsaki kan murnar yakar cutar da Najeriya ta yi.

Sannan ya jaddadawa ‘yan Najeriya cewa jami’an hukumar za su ci gaba da matsa kaimi wajen yin rigakafin magance cutar saboda gudun sake bullar ta a nan gaba.

Shuaib ya ce duk da cewa bayyana Najeriya a matsayin kasar da ta yaki cutar yana nufin ba sauran wani dake dauke da cutar a Najeriya, amma hakan ba zai sa ta daina kokarin da take yi ba.  A cewarsa akwai hanyoyi da dama da cutar za ta iya sake bulla a Najeriya, adon haka hukumomi ba za su yi kasa a gwiwa wajen bin hanyoyin dakile cutar ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *