Muhammad Babandede

Hukumar kula da masu shige da fice ta Najeriya ta ce jami’an ta sun kama tare da maida wasu ‘yan kasar Kamaru da suka shigo Najeriya ba bisa ka’ida ba a Ikot Obong dake jihar Cross River.

Mai Magana da yawun hukumar Sunday James, ya bayyana haka, ya ce runduna ta musamman da ke aikin maida ‘yan kasashen ketare ta kama mutanen a lokacin da suke kokarin shigowa Najeriya ta kwale-kwale a karamar hukumar ta Akpabuyo, dake jihar.

Ya ce nan take aka tare mutanen sun 7 sannan aka gaggauta sa su koma kasar su ta Kamaru cikin gaggawa.

James ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane da dama cikin ‘yan kwanakin nan a jihohin Cross River da Akwa Ibom da suka shigo Najeriya ba bisa ka’ida ba tun bayan umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na kulle iyakokin kasa.

A baya bayan nan ma shugaban hukumar na kasa Muhammad Babandede, ya bukaci jami’an hukumar su kara matsa kaimi tare da rangadi da tabbatar da tsare kan iyakokin kan tudu da na ruwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *