SADIYA UMAR FAROUQ
MINISTAR JINKAI TA NAJERIYA

Gwamnatin tarayya ta ce ranar Talata 30 ga watan Junin nan da muke ciki a matsayin ranar da za ta yaye ma’aikatan shirin rage zaman kashe wando na N-Power kashi na farko.

Ministar kula da harkokin jinkai Sadiya Umar Farouq ta sanar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja.

Ta ce gwamnatin tarayya ta fitoda shirin ne a shekarar 2016 karkashin shirin fidda ‘yan kasa daga kangin talauci da kuma inganta rayuwar al’umma tare da zuba jari.

Ministar ta ce a ranar Juma’a 26 ga watan Yuni za a bude kofa ga sabbin wadanda suke so su shiga cikin shirin a rukuni na 3.

Ta ce yanzu haka gwamnatin tarayya na duba yuwuwar samawa matasan dake cikin shirin su kimanin 500,000 guraben aiki a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *