CHRIS NGIGE
MINISTAN LAFIYA

Gwamnatin tarayya ta saki naira billiyan 4 da milliyan dari 5 ga Asibitoci koyarwa da cibiyoyin kula da lafiya 31 a fadin Najeriya domin biyan kudaden inshora.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige tare da ministan lafiya Osagie Ehanire suka sanar da haka a lokacin da suka yi jawabin hadin gwiwa ga manema labarai na fadar shugaban kasa dake Abuja, jim kadan bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ngige ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen biyan alawus-alawus na watannin Afrailu da Mayu, yayin da nan gaba kadan za a saki kudaden da za a biya albashin Yuni.

Ya ce kudaden na daga cikin bukatun da kungiyar likitocin cikin gida da suka tsunduma yajin aiki suka gabatar a matsayin sharadi kafin su koma bakin aiki.  

A nasa jawabin ministan lafiya Ehanire, ya bayyana tabbaci cewa likotocin za su janye yajin aikin dan komawa bakin aiki, tare da maido da kwarin gwiwa da bangaren lafiya ke da shi a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *