GARBA SHEHU

Fadar shugaban kasa ta kalubalanci rahoton da wata cibiyar kula da ‘yan cin addinai a kasar Burtaniya ta fitar inda take cewa gwamnatin tarayya ta bar masu ikirarin jihadi na kashe tare da daidaita mabiya addinin Kirista a Najeriya.  

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya ce rahoton da cibiyar ta fitar ya nuna cewa kwata-kwata ba ta san abubuwan dake ma faruwa a Najeriya ba.

Ya ce an dau tsawon shekaru da wannan barazanar ta tsakanin addinan Musulunci da Kiristanci a Najeriya, da kuma a tsakanin manoma da makiyaya.

A cewarsa ana samun rikice-rikice da dama a fadin kasar nan ne sakamakon yawan jama’ar da take da shi, da kuma wasu abubuwa makamantan haka dake haddasa sabanin.

Shehu ya kara da cewa a shekaru da dama da suka gabata, shugaban Najeriya wanda Musulmi ne da mataimakinsa Kirista sun dukkufa wajen tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *