Hukumar kula da harkokin matasa da wasanni ta fitar da dokoki da ka’idojin kariya da hukumomin shirya wasanni za su cika kafin maido da harkokin wasanni a Najeriya.

Takardun da hukumar ta fitar sun bayyana cewa ya zama wajibi bangaren wasanni su cika ka’idojin kariya na ‘yan wasa da sauran su daga cutar korona.

Kwamitin sanya ido, bincike tare da fitar da tsare-tsare na hukumar ya fitar da ka’idojin wanda ya bukaci kafa ire-iren kwamitocin a dukkanin cibiyoyin kula da wasanni na jihohi.

Sannan ya bukaci a tabbatar da an tsaftace tare da samar da ruwan mai gudana da kuma feshin kayayyakin da a baya ake amfani dasu wajen gudanar da wasannin a matakai daban-daban.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *