Daga Dr. Bello Galadanchi Wata majiya mai karfi ta kwarmata wa Radiyon Talaka cewa gwamnatin Buhari na shirin kama duk wani mai sukar Buharin akan shafukan sada zumunta.

Wannan ya zo kwanaki kalilan ne bayan sako shugaban Gamayyar Kungiyoyin Arewa, Nastura Ashir Shariff, wanda aka kama shi aka kulle biyo bayan zanga-zangar lumana da ya shirya a jihar Katsina saboda kashe talakawa da ake tayi a kauyuka da garuruwa daga ‘yan bindiga da tsakar rana. Tsarewar ta jawo Allah wadai daga kungiyoyin kare hakkin bil adama musamman Amnesty International.

Majiyar da ta nemi a sakaye sunan ta saboda dalilan tsaro, ta bayyana cewa gwamnatin ta riga ta dauki sunayen mutane, musamman matasa dake kalubalantar mulkin Buhari akan shafukan sadarwa irin su Facebook, Instagram da Twitter.

Idan ba’a manta ba, a watannin baya an kama wani mai rubuce-rubucen sukar gwamnati mai suna Dadiyata wanda har yau ba’a san inda yake ba.

A kwanakin bayannan dai Buhari yana cigaba da shan suka daga hannun jama’a a duk fadin arewacin Najeriya saboda tabarbarewar tsaro, inda ‘yan bindiga suke yawo da rana tsaka a kauyuka suna kashe mutane, suna yin fyade, suna kona gidaje da sace-sace ba tare da samun kalubale ba.

Ra’ayoyin jama’a yanzu ya rabu sosai akan shugabancin Buhari, saboda an yi masa kyakkyawan zato wajen tabbatar da tsaro a Najeriya, saboda kasancewar sa tsohon soja wanda ya tabbatar wa jama’a lokacin yakin neman zabe cewa zai kawo karshen rashin tsaro a kasar baki daya.  

Masana da kwararru sun bayyana wannan mataki, idan har aka aiwatar da shi, a matsayin toye hakkin bil adama da hana jama’a fadar albarkacin bakin su, wanda yana daga cikin ‘yancin ‘yan kasa a cikin kundun tsarin mulkin Najeriya.

Ra’ayoyi 3

Your email address will not be published. Required fields are marked *