Tsohon shugaban hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa shiyyar Legas, Hyginus Omeje, ya ce hukumar ta kama mutane dubu dari 3 da 33 da dari 8 da 99 da suka saba dokokin hanya a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019 da yake shugabantar hukumar.

Omeje, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mika jagorancin rundunar ga sabon kwamandan jihar Olusegun Ogungbemide.

Omeje wanda ya samu karin girma a hukumar zuwa mataimakin Corps Marshal, ya ce ya bada gudunmawa sosai wajen tabbatar da ana bin dokokin hanya a jihar.

Ya kara da cewa a tsawon lokacin, jami’an hukumar sun tsare, tare da kalubalantar wadanda suka saba dokokin hanya dubu 25 da dari 4 da 54.

Sannan a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, ta gudanar da gangamin wayar da kan masu saba dokokin hanya dubu dari da 26 da dari 2 da 35, kamar yadda hukumar ta umurta.

Ya kuma nuna tabbaci cewa sabon shugaban hukumar na jihar yana da kwarewar da ake bukata da zai yi aiki daidai da yadda dokar kasa ta tanada.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *