Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana Najeriya da Kamaru a matsayin kasashen da suka yaki cutar shan-inna baki daya.

Hukumar ta WHO ta bayyana hakan ne a shafin twitter na ofishinta dake kula da nahiyar Afrika wanda ke birnin Brazzaville na kasar Congo.

Ta ce wannan lokaci ya kasance mai tarihi ga kasashen da nahiyar Afrika da kuma shirin kawar da cutar shan inna na duniya.

Shima babban daraktan ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko ta Najeriya Faisal Shuaib, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin twitter ya bayyana yakar cutar da Najeriya ta yi a matsayin abin tarihi.

Ya ce hukumomi za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasar da babu mai dauke da cutar shan inna ko guda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *