Hukumar wayar da kan al’umma ta Najeriya NOA, ta bukaci gwamnatocin jihohi su ci gaba da wayar da al’umma kan hanyoyin kaucewa da kamuwa da cutar korona, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurta.


Shugaban hukumar na kasa Garba Abari, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce wayar da kan al’umma da ilmantar dasu ne ginshikin shawo kan yaduwar annobar a sassan Najeriya.

Abari ya kuma jinjina kokarin da hukumarsa ke yi wajen yaki da yaduwar cutar, sai dai ya nuna takaici bisa yadda bata samun goyon bayan da ake bukata daga gwamnatocin jihohi.

Sannan ya yabawa wasu daga cikin gwamnatocin da ma’aikatu da suka aminta da muhimmancin da hukumar take dashi wajen yawarwa tare da ilmantar da kan al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *