Ministar kula da harkokin mata da walwalarsu Pauline Tallen, ta jaddada kudurin gwamnatin tarayya na shawo kan matsalar cin zarafi ta hanyar fyade a Najeriya.

Ministar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta fasahar zamani da wakiliyar majalisar dinkin duniya Dayo Israel, da wata kungiya ta kasar Burtaniya suka shirya.

Ta ce ya zama wajibi a hada hannu wajen ilmantar da ‘ya’ya masa da kuma magance matsalar cin zarafi dake da alaka da fyade da ake yawan samu yanzu a Najeriya.

Tallen ta ce ilmantar da ‘ya’ya mata da kuma magance matsalar cin zarafi na daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta fi maida hankali akai yanzu.

Ta kuma lissafo cin zarafi, fyade yara kanana, rashin daidaito da kuma karancin wakilci a siyasa da gwamnati a matsayin abubuwan dake ciwa mata tuwo a kwarya a Najeriya.

Ministar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci rundunar ‘yan sanda da ma’aikatar shri’a da su tabbatar da an hukunta wadanda aka samu da laifin fyade a fadin kasar nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *