MUHAMMADU BUHARI
SHUGABAN NAJERIYA

Kwamitin yaki da cutar korona na Najeriya ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa gudunmawar shawarwari da kuma jagoranci mai kyau da zai taimaka a yaki da cutar.
Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana hakan a jawabin kwana-kwana da kwamitin ke yi a Abuja.
Mustapha ya ce shugaba Buhari ya bada muhimmiyar gudunmawa a aikace-aikacen kwamitin na yaki da cutar a fadin Najeriya.
Ya ce goyon bayan da gudunmawa da kwamitin ya samu daga shugaba Buhari na da matukar muhimmanci kuma ta taimaka a yaki da take da cutar dake da saurin yaduwa.
Sannan ya yabawa kungiyar gwamnoni ta Najeriya da hadin gwiwa da kwamitinsa ya samu daga sauran wasu kwamitoci da aka kafa a matakai daban-daban domin yaki da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *