Babban attoni janar na kasa, kuma Ministan Shariah Abubakar Chika Malami SAN. Ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya gaggauta sauke Labaran Magu daga kan kujerarsa ta shugaban hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC.

A rahoton da Chika Malami SAN, ya aikewa shugaban kasa inda ya bukaci a tumbuke Magu daga shugaban EFCC, Malami, ya zargi Magu da kwashe kudaden da aka kwato daga hannun mutanan da suka kwashi dukiyar kasa ba bisa ka’ida ba.

Wato dai, ana sake sace kudaden satar da ake kwatowa a hannun barayin da suka debi dukiyar Gwamnatin. Tamkar dai Kace sata ce take sake sauya hannu.

Allah ya jikan tsohon shugaban EFCC na farko, Malam Nuhu Ribadu, ba Dan ya mutu ba. Shi ne mutumin da tsohon Gwamnan Delta James Ibori ya baiwa cin hancin Dalar miliyan 15 kimanin Naira biliyan 3 a lokacin, Amma saboda gaskiya da tsoron Allah Nuhu Ribadu ya kai kudin babban bankin kasa CBN.

Irin su Nuhu Ribadu sune kalilan din mutane da gaskiya da rikon amanarsu ta bayyana. Kuma irinsu ya dace al’umma su sanya a gaba domin fitar mana da suhe daga wuta.

Indai ana yaki da cin hanci da rashawa na gaskiya, zamu ga yadda shugaban kasa zai yi aiki da shawarar rahoton Chika Malami SAN. Daman Hausawa sunce ko wane gauta ja ne.

Shugaban kasa dai yayi rantsuwa da Allah cewar zai yi gaskiya, kuma zai Yaki cin hanci da rashawa. Ya kuma taba fadar cewar, “Ni ba zan ci hanci ba, kuma ba zan ga ana cin hanci na yi shiru na kauda kai ba” Allah yasa wannan maganar ta zama hujja ga shugaban kasa, ba hujja akansa ba.

Yasir Ramadan Gwale
19-06-2020

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *