Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya ce ofishinsa ya fara shirye-shiryen kafa kotu na musamman da zai rika yanke hukunci kan laifuffukan fyade da cin zarafin jinsi.

Malami ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na hadin gwiwa da sakataren hukumar kare hakkin bil’adama Tony Ojukwu.

Ya ce ma’aikatar shari’a ta fara duba dokoki da bincike mai zurfi domin duba yiwuwar kafa kotun tare da tabbatar da ana hukunta duk wanda aka samu ya aikata laifin cikin hanzari.

Malami wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Dayo Apata, ya ce an dade ana tattauna yadda za a tabbatar da hukunta duk wadanda aka samu da aikata ire-iren laifukkan.

Ya ce kafa kotun zai taimaka wajen hukunta duk wanda aka kama, ba tare da daukar lokaci mai tsawo ba, kuma hakan zai zama tamkar izina ga wadanda ke shirin aikata laifin.

Ministan ya kara da cewa akwai shirye-shirye da ake na yiwa duk wadanda aka samu da laifukan fyade da cin zarafin jinsi rijista a ofisoshin ‘yan sanda dake fadin kasar nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *