Osagie Ehanire
Ministan Lafiya na Najeriya

Ministan kula da harkokin lafiya Osagie Ehanire, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun karin mace-mace sakamakon yawaitar masu kamuwa da cutar korona.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron kwana-kwana da kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan yaki da cutar ke shiryawa a Abuja.

Ya ce akwai matakai da gwamnatin tarayya ke dauka na tabbatar da an rage masu kamuwa da cutar da kuma wadanda take kashewa.

A cewar Ehanire za a ci gaba da karfafawa cibiyoyin kula da masu dauke da cutar gwiwa su rika amfani da magungunan da aka tabbatar suna taimakawa wajen samun saukin wadanda suka kamu da cutar.

Jami’in kwamitin yaki da cutar Sani Aliyu, ya ce har yanzu ba a ci karfin kawo karshen cutar korona a Najeriya ba, saboda haka akwai bukatar mutane su yi taka-tsan-tsan.

Ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakin sassauta dokar hana fita da aka sanya ne domin ba ‘yan Najeriya damar ci gaba da neman abinci, musamman wadanda sai sun fita suke samo abin da za su ci a rana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *