Nasir Ahmad El-Rufai
Gwamnan Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar kara sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar matukar al’ummomi suka ci gaba da saba dokokin kariya.

Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana haka, a lokacin da yake kaddamar da cibiyar gwajin cutar ta tafi da gidan ka da kungiyar USAID ta kasar Amurka ta ba jihar.

Ya ce sakamakon yawaitar masu dauke da cutar wanda ke kokarin zarta adadin wadanda ya kamata ma’aikatan lafiya a jihar su kula da su, za a sake sanya dokar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar a baya ta dage dokar takaita zirga-zirgan ce sakamakon tabbaci da take dashi na isassun kayayyakin aikin gwajin masu cutar.

Sannan ya roki al’ummomin jihar da su ci gaba da bin ka’idoji da kwararru kan harkokin lafiya suka bada, tare da kaucewa yawan fitan da babu gaira babu dalili.

Ya kara da cewa idan bukatar sake sanya dokar takaita zirga-zirga ta taso, gwamnatinsa za ta gaggauta daukar matakin hakan domin gujewa yawaitar yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *