Boss Mustapha
Shugaban Kwamitin Yaki da Korona

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da yin taka tsan-tsan da daukar matakan kariya daga cutar korona a daidai lokacin da damina ke ci gaba da kankama.

Shugaban kwamitin yaki da cutar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa Boss Mustapha ya bada gargadin a lokacin da yake jawabi kan irin nasarori da kwamitinsa ya samu.

Ya ce lokacin damina na zuwa da sanyi da tari da mura wadanda duk alamu ne na kamuwa da cutar korona.

Mustapha wanda shine sakataren gwamnatin Najeriya ya yi gargadin cewa a lokaci irin wannan na damina an fi hadarin kamuwa da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *