A jiya ne dai aka yi ta yada jita-jita tsohon Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya rasu, wanda har surikar sa kuma ‘yar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ke auren dansa Idris Ajimobi ta mayar da martani a shafinta na Tiwita kamar haka:

Abinda ta ke cewa da Hausa shine, “Godiya game da sakonnin ku, amma Babanmu har yanzu yana raye, Mun gode wa Allah. Idan kuma lokacinmu yayi, to duk sai mun mutu, saboda haka fara jira tukunna…

To amma daga baya majiyoyi masu karfi sun tabbatar wa Radiyon Talaka cewa tsohon gwamnan ya shiga halin suma ne sakamakon cutar korona.

Inda aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a Ikoyin jihar Legas, wajen da tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Marigayi Malam Abba Kyari ya yi jinyar cutar Korona har ya rasu.

Wasu majiyoyin sun ce Ajimobi ya farfado amma yana ci gaba da karbar magani a dakin jinyar marasa lafiya masu bukatar kulawar musamman ta gaggawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *