Wani mutum ya samu tarin magoya baya akan yanar gizo biyo bayan bayyana wa duniya cewa ya kebe kanshi na kwanaki 75, in da ya dawo tare da yin tambaya mai jan hankali akan kafar tiwita.

Daniel Thorson ya kebe kanshi da al-umma ne a can cikin wani dan karamin bukka a cikin daji a jihar Vermont dake arewa maso gabashin Amurka, inda ya gudanar da ibada irin ta masu bin addinin budda tun watan Maris.

Thorson wanda aka sanshi a matsayin mai rubuce rubuce akan yanar gizo da nazarin rayuwa ya katse duk wata muamala daga duniya, ba tare da jin labarai ba, shine ya bude shafin tiwita inda ga yadda duniya take da kokarin kalubalantar annobar Korona.

Labarin shi ya samu shahara ne saboda jama’a da yawa na tunanin ko wadanni manyan tambayoyi yake da su, da kuma martanin da zai biyar game labaran abubuwan da suka faru a duniya a lokacin da yake ibada, bacci, takawa a kasa da cin abinci shi kadai a cikin daji.

Wasu da yawa sun masa barkwance suna cewa babu abunda ya canza, wasu kuma sun ce “ya yi rashin samun damar ganin duniya ta sha kwaya”.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *