Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce bai gamsu da kokarin da manyan hafsoshin tsaro ke yi na yaki da ‘yan ta’adda a wasu yankunan kasar nan ba.

Mai ba shugaban kasa Shawara kan harkokin tsaro Babagana Mongunu ya bayyanawa manema labarai haka.

Ya ce shugaba Buhari ya ce ba zai sake sauraren hafsoshin tsaron ba har sai sun yi nasara a yaki da ake da ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Shugaba Buhari, dai ya yi ganawar musamman da manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ne a fadarsa da ke Abuja.

Ganawar ta zo ne bayan kasar Amurka ta soki Nijeriya a kan yadda ‘yan ta’adda ke kashe mutane a yankin Arewa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *