Muhammad Sa’ad Abubakar III
Sarkin Musulman Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya ce matsalar taɓarbarewar tsaro a yankin Arewacin Najeriya abin tashin hankali ne.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar Jama’atul Nasril Islam ta rabawa manema labarai a Kaduna.

Sarkin Wanda shine shugaban kungiyar na kasa ya nuna takaici bisa zubar jini da lalata dukiyoyin jama’a a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Jihar Neja.

Sarkin ya ce ya zama wajibi gwamnati ta kara matsa kaimi wajen kawo karshen matsalar da ta addabi yankin.

Basaraken ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ɗaukar matakan tura jami’an soji yankin dake fama da rikicin domin kai ɗauki.

A cewarsa akwai bukatar gwamnati ta gudanar da bincike sosai akan batun harkar tsaro sakamakon ƙorafin da ake dashi na wasu jami’an tsaro suna mai da harkar haryar samun kudaden shiga.

Sannan ya bukaci al’ummomin Najeriya su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin Allah kawo ƙarshen matsalar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *