Abdulmumini Kabir Usman
Sarkin Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman ya ce makiya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ke yiwa gwamnatinsa zagon kasa.

Sarkin ya bayyana hakan ne ya yin da yake magana da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguna.

Ya ce ya sha fada wa Shugaba Buhari ya rika taka-tsantsan da makiya da ke ciki da wajen gwamnatinsa.

Sarkin ya ce makiyan ne suke kokarin haifar da matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya saboda a ga gazawar gwamnatinsa.

Tawagar da ta hada da Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu, Shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi da Shugaban Hukumar Tattara bayanan sirri, Ahmed Rufai sun ziyarci Katsina ne don yin jaje, tare da tattaunawa Kan sabbin matakai da za a dauka bisa kisar da yan bindiga suka yi a baya bayan nan.

Tawagar ta ce gwamnatin shugaba Buhari na iya kokarin ta wajen ganin ta magance kallubalen tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *