Jami’an tsaro sun sako wanda ya jagoranci zanga-zangar nuna adawa da ayyukan ta’addancin dake faruwa a jihar Katsina Ashiru Shariff Nastura.

Jami’an tsaro sun kama Nastura ne biyo bayan zanga-zangar da ta haifar da suka ga gwamnatin jihar da ta tarayya kan rashin daukar matakan da suka kamata wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Jim kadan bayan kamashi’ al’ummomi da kungoyoyi da dama ne dai suka rika kiraye-kirayen jami’an tsaro su gaggauta sakinsa, saboda a cewarsu bai saba dokar kasa ba.

Tuni dai shugaba Buhari ya aike da tawaga ta musamman zuwa jihar ta Katsina domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *