An rufe ginin Majalisar Tarayyar Najeriya dake Abuja saboda fargabatar yaduwar cutar korona. Ana shirin yiwa ginin feshin magani.

Wata sanarewa mai lamba NASS/HR/MSD/ClR/003/IV138 tace za’a rufe ginin na kwanaki biyu.

Wannan rufewa dai ya sa an fara zargin ko dai Korona na yaduwa ne a cikin majalisun.

Idan ba’a manta ba, gwamnatin Jihar Legas ta nuna alamun cewa Sanata Sikiru Adebayo Osinowo ya rasu ne sakamakon cutar Korona.

Dan majalisar wanda aka fi sani da “yaji” ya rasa ransa ne a asibitin First Cardiologist bayan gajeruwar rashin lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *