MUHAMMADU BUHARI
SHUGABAN NAJERIYA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci ministoci da ke kula da harkokin tsaro su fito da sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a Nijeriya.

Tuni dai ministocin su ka gana a babban birnin tarayya Abuja da nufin sauke nauyin da shugaban kasa ya rataya a wuyan su.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya aike da tawaga ta musamman karkashin jagorancin mai bashi sahwara kan harkokin tsaro Babagana Monguno, zuwa Katsina.

Sannan ya bukaci ‘yan majalisar zartarwa ta kasa su zage dantse wajen tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi jihar Katsina da sauran jihohin da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *